Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa ya sami hotunan abubuwan da suka faru bayan yunkurin kissa Firai ministan wanda bai sami nasara ba. Labarin ya kara da cewa tuni dai wadanda suka kai masa harin sun sulele sun shiga daji, amma an tura jami'an tsaro don gano inda suke.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa wannan harin yana zuwa ne a dai dai lokacinda firai ministan yake cewa zai yi watsi da duk wata shawarar da majalisar gabacin kasar zata yanke kan al-amuran kasar a yau Alhamis.
342/